Connect with us

News

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sha rantsuwar kama aiki

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sha alwashin karfafa dangantakar diflomasiyya da sauran kasashen duniya a yayin da ya dauki alkawarin inganta tattalin arzikin Turkiyya.

Zababben shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sha alwashin karfafa dangantakar diflomasiyya da sauran kasashen duniya a yayin da ya dauki alkwarin kara inganta tattalin arzikin kasar, tare da samar da sabbin sauye-sauyen da za su ciyar da kasar gaba.

Firaministan kasar Indiya ya ci alwashin hukunta masu sakaci a haɗarin jiragen ƙasa

Erdoghan ya fadi hakan ne bayan shan rantsuwar shugabancin kasar a sabon wa’adin mulki a karo na uku a wannan Asabar a sakamakon nasarar da ya samu a zagaye na biyu na zaben kasar da ya gudana a makon da ya gabata. Shugabannin kasashen duniya akalla 21, da firaminista 13 ne ke halartar bikin shan rantsuwar na Erdogan a birnin Ankara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending