Connect with us

News

Yanzu yanzu: Tinubu ya umarci hukumomin tsaro a Kano su dakatar da rushe shagunan da gwamnati ke iƙirarin an gina ba bisa ƙa’ida ba.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tsoma baki kan rusa gine-ginen da ake yi a Kano bayan ganawarsa da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Advertisement

Idan dai za a iya tunawa Gwamna Abba Kabir Yusuf a cikin daren ranar Asabar ya rusa wasu gine-gine a Otal din Daula da kuma sansanin Hajji da ke cikin birnin Kano.

Rikicin Shugabanci Ya Kunno Kai A Majalissar Dokokin Jihar Nasarawa

Gine-gine na miliyoyin nairori sun lalace kamar dai yadda gine-gine masu hawa uku na farko da shaguna 90 a kan titin Race Course, a unguwar GRA ta Nasarawa, wanda ke nuna mafarin gine-ginen da gwamnati ta kira haramtacce.

Advertisement

A ranar Asabar ne Gwamna Yusuf ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da rusa gine-ginen da gwamnatin ta yi imanin cewa haramun ne a jihar.

Wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce za a ci gaba da aikin rusau.

Advertisement

Idan dai ba a manta ba tsohuwar gwamnatin Ganduje ta ce ginin da aka gina a Otal din Daula shiri ne na hadin gwiwa na jama’a.

Wani mai gina kadarori mai suna Lamash Properties Limited, ya sha alwashin kalubalantar rushe otal din Daula da gwamnatin jihar Kano ta yi inda ya bukaci a saka jarin N10bn a aikin.

Advertisement

LAMASH Properties Limited, wani kamfani ne na raya kadarori da gwamnatin jihar Kano ta gayyace shi tare da wasu kamfanoni a wasu lokutan a karshen shekarar 2020 domin neman sake gina tsohon otal din Daula a karkashin wani kamfani mai zaman kansa (PPP).

Bayan faruwar lamarin, Gwamna Ganduje ya garzaya don ganawa da shugaban kasar a ranar Litinin a fadar shugaban kasa domin yi masa bayani kan lamarin.

Advertisement

Jaridar Politics Digest ta rawaito cewar majiyoyin fadar Villa, shugaban ya damu matuka da asarar biliyoyin Naira da wasu mutane suka yi saboda rugujewar ginin.

“Tinubu ya ba da umarnin a dakatar da rushewar saboda rashin hankali ne kuma yana haifar da asara ga ‘yan Najeriya,” in ji majiyar da ta so a sakaya sunanta.

Advertisement

Ya kuma bukaci jami’an tsaro da su dakile duk wani barna a Kano.

Majiyar ta kara da cewa, “Wannan ne ya sa gwamnan ya tsaya da rugujewar da ake yi saboda rahoton tsaro da jami’an tsaro suka gabatar masa.

Advertisement

Da aka tuntubi ko gwamnati za ta ci gaba da rusa ginin, Tofa ya shaida wa jaridar cewa: “har yanzu ana ci gaba da rusau, gwamnati ta kuduri aniyar kwato kadarorin jama’a da aka sayar ko aka ware.”

Ya kara da cewa, “Wannan aikin yana da matukar amfani ga jama’a, za a kai ga cimma matsaya mai ma’ana in sha Allahu,” in ji shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending