News
An gurfanar da Wani malamin Primary da laifin fashi da makami
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wato kotun majestiri da ke Makurdi babban birnin jihar Benue ta ba da umarnin tasa ƙeyar wani malamin firamare zuwa gidan yari sakamakon zargin sa da laifin fashi da makami.
An dai gurfanar da malamin mai suna Emmanuel Okoriko, ɗan shekara 33 da laifin fashi da makami.
Yan Majallisar Dokokin Jihar Kano Zasu Karbi Horon Sanin Makamar Aiki
Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ruwaito cewa, ‘yan sanda sun zargi Emmanuel Okoriko mazaunin garin Otukpo da wannan laifi na fashi da kuma yunƙurin hallaka ɗan Adam.
Alƙalin kotun mai shari’a Roseline Iyorshe, ta ki amincewa da hanzarin da wanda ake zargin ya gabatar, inda nan take ta bada umarnin tura shi gidan yari..
Tun farko ɗan sanda mai shigar da ƙara, Sifeta Jonah Uletu, ya shaidawa kotun cewa, wani mai suna Kelvin Ikwue ya shigar da ƙorafi ga ‘yan sanda cewa, a ranar 23/05/2023, wani mai suna Emmanuel Okoriko, ya yi wa mahaifinsa mai suna Adakole Ikwue fashi da makami, inda ya yi amfani da sukuldireba ya kai mishi farmaki.
A cewar sa wanda ake zargin ya cakawa mahaifinsa sukuldireba a wuya sannan ya sace masa wayarsa ƙirar Samsung Galaxy wadda kuɗinta ta kai Naira 165,000
