News
Gwamnatin Buhari Ta Barnatar Da Dala Billiyan 19 Kan Gyaran Matatun Mai
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kashe sama da dala biliyan 19 kwatankwacin abunda akayi amfani da shi wajen gina matatar man dangote wajen gyara da matatun man Najeriya.
Gwamnatin Buhari a cikin shekaru 8 ta bada kwangilar gyaran matatun mai na Kaduna da Fatakwal, da Warri amma babu wadda ke aiki har kawo yanzu, yayin da Dangote ya gina mafi girma a Afirka cikin kasa da shekara 5.
Da yake magana a gidan Talabijin na kasa a jiya, Gwamna Sule ya ce matatar Dangote ta ninka matatun man da muke dasu guda uku idan aka samar da ita akan dala biliyan 19.
Gwamnan APC ya koka da cewa gwamnatin Buhari bata gina wata sabuwar matatar mai ba, amma an kashe sama da dala biliyan 19 wajen gyaran matatun mai guda uku a cikin shekaru takwas kuma babu wani abu da aka gani a kasa.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
