News
Hukumar EFCC Ta Saki Ortom Bayan Sa’o’i 10
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An saki tsohon gwamna Samuel Ortom na jihar Benue daga hannun hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC.
Jaridar daily trust ta ruwaito yadda tsohon gwamnan ya amsa gayyatar hukumar da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Talata.
Ya shiga cikin ofishin shiyya na Makurdi na hukumar, wanda ke kan titin Alor Gordon a babban birnin jihar, tare da rakiyar wasu tsoffin IDES dinsa guda biyu.
Mataimakin tsohon gwamnan kan harkokin yada labarai, Terver Akase, da kuma babban mataimakin na musamman kan ayyuka na musamman, Abraham Kwanhgu, an gansu tare da shi.
Jami’an ‘yan sanda sun gana da Ortom kan kashe kudaden da Benue ta yi a karkashinsa.
Daya daga cikin masu taimaka masa, wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya shaida wa manema labarai a wajen ginin hukumar cewa babu wani abin fargaba.
A yayin zaman majalisar ministocinsa da aka gudanar a tsohon dakin liyafa na gidan gwamnati, Makurdi, Ortom ya bukaci ‘yan majalisarsa da kada su ji tsoro a duk lokacin da EFCC ta gayyace su don amsa tambayoyi.
Ortom ya shaidawa mambobin majalisar ministocinsa cewa shi ba matsoraci ba ne da zai gudu daga EFCC.
