DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Yan sandan kasar nan tayi kira ga wadanda wani mai shirya bidiyon tsokana a intanet ya ritsa da su, da su fito su kai rahoto kan irin halin da ya suka shiga.
Trinity Guy yana yin bidiyo wanda ya ke wallafawa a sahfukan sada zummunta inda ya ke da dubban masu bibiyan shi. Wasu daga cikin bidiyon da ya ke yi sun nuna shi ya yi kamar an harbe shi, hakan na girgiza masu wucewa da ba su ji ba ba su gani ba.
“Ina ganin yakamata a kama mutumin. Ya kamata mutanen da ke samun fargaba ta dalilin bidiyon ya kamata su rika ba kai rahoton ‘yan wasan barkwanci saboda yawancin ayyukansu na aikata laifuka ne, fasikanci, da kuma mugunta,” in ji kakakin ‘yan sanda Olumuyiwa Adejobi.
BBC Hausa ta rawaito cewa “Wadannan matan na da dalilin shari’a sosai a kansa.”
Wasu a yanar gizo sun mayarwa ‘yan sanda martani, suna masu cewa kamata ya yi rundunar ta yi maganin cin zarafi da da rashawar da ta janyo zanga-zangar EndSars ta Najeriya.
