Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Cire Kudaden Yan Fansho

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusif ya bada umarnin dakatar da cire wasu kudi naira 370 daga albashin Ma’aikata.
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin daina cire kudin Yan fansho inda ake baiwa wani kamfani mai suna Share Benefit Investment Limited.
A takardar umarnin dakatarwar da sakataren gwamnatin Kano Abdullahi Baffa Bichi ya sanya wa hannu mai dauke da kwanan watan 19 ga watan Yuni 2023, ta umarci shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da shugaban Ma’aikatan jihar Kano da shugaban hukumar Yan fansho da kuma shugabannin kananan hukumomi da sauran shugabannin hukumomin gwamnati da su tabbatar an daina yanke wancan kudi naira 370.

Wata Mata Ta Haihu A Cikin Jirgin Lagos Zuwa Netherland

Gwamnan yace tsarin yanke kudin daga hakkokin Ma’aikata tare da baiwa wani kamfani mai zaman kansa haramtacce ne, a don haka gwamnatin Kano ta dakatar dashi ba tare da bata lokaci ba.
Tun bayan zamansa gwamna Abba Kabir Yusuf, ya fara da sauye da sauye musamman cire harajin da babu gaira babu dalili da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta Ƙaƙabawa mutanen jihar.
Hakan ya sanya farin ciki a zukatan jama’a da dama, domin kuwa a baya suna biyan harajin ne ba don son ran su ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending