News
Wata Mata Ta Haihu A Cikin Jirgin Lagos Zuwa Netherland
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Jirgin KLM da ya nufi kasar Netherland ya yi saukar gaggawa a kasar Spain tare da karin fasinja bayan wata mata ta shiga nakuda ba zato ba tsammani.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya rawaito cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aviation24 a ranar Talata cewa, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin, inda daya daga cikin fasinjojin da ke cikin jirgin KLM mai lamba 588, kirar Boeing 777, ya samu nakuda a lokacin da ya taso daga Legas zuwa Amsterdam na kasar Netherlands.
Gwamnan Kano Ya Nada ‘Dansa’ Shugabancin Wata Hukumar Gwamnati
Matar wadda ba a bayyana sunanta ba, an bayyana cewa an kai ta ne zuwa galey din gaba inda ta haifi diya mace da wuri. Daga nan sai jirgin ya yi saukar gaggawa a Barcelona inda ma’aikatan lafiya ke jira.
An ce duka uwa da ‘yar suna cikin koshin lafiya.
Mai magana da yawun KLM, Marjan Rozemeijer, a ranar Talata, ta ce, “Zan iya tabbatar da cewa an haifi jariri a kan KL 588 akan hanyarsa daga Legas zuwa Amsterdam, saboda dalilai na sirri ba zan iya yin wani karin bayani game da haihuwar ba.
