News
Kungiyar Kwadago NLC Ta Nuna Kin Amincewarta Kan Karin Kudin Lantarki A Najeriya.

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta gargadi mahukunta akan shirin kara kudin wutar lantarki a kasar Shugaban kungiyar, Joe Ajaero shi ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni Ya ce karin kudin wutar a irin wannan lokaci bai kamata ba duba da yadda yanayin kasar take
Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta soki shirin da ake yi na kara kudin wutar lantarki da kashi 40 a ranar 1 ga watan Yuli. Kungiyar ta ce yin hakan bai kamata ba a irin wannan lokaci ba, wanda ya nuna rashin kulawa ga kwastomominsu musamman talakawa.
Cire Tallafi: Dole ‘Yan Siyasar Najeriya Su Sadaukar Domin Talakawa
Shugaban kungiyar, Joe Ajaero shi ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni, cewar Punch. NLC ta bayyana shirin karin kudin wutar lantarki a rashin dacewa
“A wannan lokaci, karin ya nuna rashin kulawa ga kwastomomi musamman talakawa. “Karin ya fayyace yadda aka kara kudin farashin litan mai da kashi 100 wanda ya kawo karin farashin kayayyaki daga kashi 16.9 zuwa 22.1. “Duk da haka, wannan bai zama dalilin da za a kara kudin wuta ba. “Duk da haka, ma’aikatar ba ta iya samar da Megawat 5000, sannan akwai kare-karen da aka yi ba tare da sanarwa ba.” Kungiyar ta bayyana rashin tabbas a farashin wutar lantarkin nan gaba Sanarwar ta kara da cewa kamar yadda Leadership ta tattaro: “Babbar matsalar shi ne rashin iya gudanar da sabon tsarin inda suka ce zuwa watan Agusta ‘yan Najeriya za su iya biyan sabon farashi.
