Connect with us

News

Babbar magana: waliyin amarya ya sace sadaki ana tsaka da daurin aure a Kano.

Published

on

Gurin dauren Aure

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Wani al’amari mai kama da almara ya faru a Kano, inda aka zargi wani waliyin amarya da sace sadaki.
An sace kudin sadaki ana tsaka da daurin aure a unguwar Kurna dake birnin Kano.

Yadda muka ƙwato Naira biliyan 454 daga hannun ɓarayin kuɗaɗen talakawa a shekaru huɗu – ICPC

Gaskiya Ta Fi Kwabo ta jiyo cewa, an dakatar da daurin aure yayin da kowa yayi cirko-cirko, bayan da aka nemi sadakin amarya aka rasa.
Sai dai wata majiya ta ce, Jim kadan da faruwar wannan lamari ne sai aka fara ‘yar caje, inda nan da nan aka samu kudin a aljihun babbar rigar waliyin amaryar.
Sai dai ya ce, shi fa bai san yadda aka yi kudin suka shiga aljihunsa ba.
Daga karshe dai an tasa waliyin amarya zuwa waje, sannan aka kira kaninsa ya maye gurbinsa, aka daura auren.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending