News
Abba Kabir Ya Dakatar Da Ma’aikatan Da Ganduje Ya Ɗauka
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya dakatar da albashin ma’aikata 10,800 da Gwamna Ganduje ya ɗauka a ƙarshen mulkinsa.
Akanta Janar na jihar Kano, Abdulkadir Abdulsalam ne ya bayyana haka a hirarsa da manema labarai.
Ya ce gwamnan ya dakatar da biyan albashin ne har sai an tantance su domin gane waɗanda suka cancata da kuma ƴan alfarma.
Abdulkadir Abdulsalam ya kuma ce duk ma’aikatan ƙananan hukumomi da tsohuwa gwamnati ta mayar ma’aikatan jiha a ƙarshen wa’adinta za su ci gaba da karɓar albashinsu na ƙaramar hukuma.
Sai dai ya umarce su da su ci gaba da aiki ma’aikatun da aka tura su na jiha har zuwa lokacin da za a tantance su domin gano makomarsu.
Akanta Janar ɗin ya kuma yi wa ma’aikata da ƴan fensho albishirin an daina yanke musu kuɗinsu kamar yadda ya ce ana yi a gwamnatin da ta gabata.
Ya kuma yi kira ga ɗaliban sakandire kusan 60,000 da tsohuwar gwamnati ta gaza biya musu kuɗin jarrabawar NECO har aka rufe rajista cewa wannan gwamnatin ta biya an buɗe shafukan intanet ɗin da za su rajista.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
