Business
Dangote ya zama mutumin da ya fi kowa arziki a Afirka, yayin da Bill Gates yake na 4 a duniya
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Shugaban Rukunin Dangote, Aliko Dangote, ya ci gaba da rike matsayinsa na attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, duk kuwa da yadda kudin Najeriya ke kara tashi da dala, kamar yadda mujallar Bloomberg Billionaires Index ta bayyana.
An kiyasta dukiyar Dangote a kan dala biliyan 15.6 a jerin fitattun attajiran da aka fitar kwanan nan a ranar Talata, inda ya sanya shi a kan gaba a jerin masu kudin Afirka a cikin Index.
Ellon Musk da Bernard Arnault su ne na farko da na biyu mafi arziki a duniya, tare da dukiyar da ta kai dala biliyan 219 da dala biliyan 194, bi da bi. Jeff Bezos ya zo na uku da dala biliyan 151, sai shugaban Microsoft Bill Gates mai dala biliyan 130, Larry Ellison ya zo na biyar da dukiyar da ta kai dala biliyan 130.
Duk da sauyin da kudin Najeriya ke da shi, martabar Dangote a matsayin wanda ya fi kowa arziki a Afirka ya nuna irin nasarorin da ya samu a harkokin kasuwanci da zuba jari a sassa daban-daban.
Wasu ‘yan Afirka biyar ne suka shiga jerin ‘yan kasuwa na baya-bayan nan na hamshakan masu kudi 500 na duniya a shekarar 2023. Sun hada da ‘yan Afirka ta Kudu Johann Rupert da iyalansa, wadanda ke da arzikin da ya kai dala biliyan 13.3, Nicky Oppenheimer, Nassef Sawiris, Natie Kirsh, da Naguib Sawiris, wanda ke da dala biliyan 9.0, dala biliyan 7.47, dala biliyan 7.37, da dala biliyan 5.93.
