News
Farashin fetur ya karye a defo na Najeriya, adai-dai lokacin da ake raɗe-raɗin karin farashin man zuwa naira 700
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Farashin fetur ya karye a defo na Najeriya, adai-dai lokacin da ake raɗe-raɗin karin farashin man zuwa naira 700 duk lita a wannan watan na Yuli.
Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya, IPMAN ta tabbatar da karyewar farashin, ta ce ana bayar da shi naira dari hudu da wani abu sabanin sama da naira dari biyar kan duk lita ɗaya.
Shugaban kungiyar reshan arewacin Najeriya, Bashir Ahmed Danmalam ya shaidawa BBC cewa farashin ya karye ne sakamakon karancin bukatarsa, kuma za a samu rangwamen farashin a gidajen mai.
“A yanzu haka man fetur a defo-defo din da suke Lagos da warri da Calabar an samu sauki domin yana kasa da naira dari hudu”.
Dan-malam ya ce farashin man zai yi kasa a kwanaki masu zuwa a sasan Najeriya daban-daban.
“Daga cikin makon da mu ke ciki farashin man zai yi kasa, sannan kuma ya kamata a san cewa yawan masu siyan man ma yaragu, ba kowa yake da kudin da zai iya siyan mai yanzu ba”.
