Connect with us

News

Majalisar wakilai ta umarci NUC ta dakatar da ƙarin kuɗin makarantar da jami’o’i suka yi nan take.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Majalisar Wakilai ta umarci hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa (NUC) ta dakatar da ƙarin kuɗin makarantar da jami’o’i suka yi nan take.
Wakilin Mazaɓar Birnin Kano, Ali Sani Madakin Gini (NNPP) ne ya gabatar da wannan ƙudirin a zauren majalisar.
Madakin Gini ya ce jami’o’in gwamnatin tarayya sun nunnuka kuɗin makaranta sakamakon hauhawar farashi da ƙarancin kuɗin tafiyarwa da suke samu daga gwamnati.

Yadda ‘yan Nijeriya ke fama da radadin cire tallafin man fetur.

Ya ce daga cikin jami’o’in da suka yi wannan ƙarin akwai Jami’ar Bayero dake Kano (BUK), Jami’ar Najeriya dake Nsukka (UNN), Jami’ar Jos, da Jami’ar Noma ta Michael Okpara.

Ɗan Majalisar ya bayyana damuwar cewa an yi ƙarin kuɗin ne lokacin da al’ummar Najeriya ke fama da tsananin talauci, rashin aikin yi, da hauhawar farashi sanadiyyar janye tallafin man fetur.

Ya ce ƙarin kuɗin jami’o’in zai kawo tarnaƙi ga karatun ɗalibai da dama da ba za su iya biya ba.

Advertisement

Bayan gudanar da muhawara, Majalisar ta amince da wannan ƙudiri kuma ta umarci NUC ta dakatar da ƙarin nan take.

Sannan ta umarci kwamitin Ilimi mai zurfi da zarar an kafa shi, ya lalubo hanyar da za a samawa jami’o’i ƙarin kuɗin shiga ba tare da an ɗora wa ɗalibai da iyayensu nauyin ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending