Connect with us

News

Majalissar Wakilai Ta Buƙaci Ƙarin Albashi, Da Alawus

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

‘Yan majalisar wakilai na neman a sake duba albashinsu da alawus-alawus, bayan cire tallafin man fetur da kuma halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Advertisement

Jaridar indaranka ta tattaro cewa bukatar ta biyo bayan ganawar da ‘yan majalisar suka yi a ranar 11 ga watan Yuli bayan sun shiga wani zama na zartarwa a zaman majalisar.

Majalisar Wakilai Na Wani Yunkuri Na Tsawaita Amfani Da Jarabawar UTME Zuwa Shekara 3

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa cikas din da ‘yan majalisar ke samu daga albashi da alawus-alawus ne ya tilastawa majalisar shiga zaman zartarwa domin duba lamarin.

Advertisement

‘Yan majalisar sun kuma bukaci shugaban majalisar, Tajudeen Abass, ya yi bayani kan dalilin samun jinkirin biyansu albashi da alawus-alawus, lamarin da ya sa wasun su shiga yin rance.

Sai dai daya daga cikin ‘yan majalisar da ya halarci taron amma ya bukaci a sakaya sunansa saboda ba a ba shi damar yin magana kan sakamakon zaman majalisar zartarwa ba, ya yi watsi da jita-jitar.

Advertisement

Da yake karyata rade-radin, dan majalisar ya ce kawai sun shaida wa shugaban majalisar cewa albashi da alawus-alawus din su ba za su iya biyan bukatar aikinsu ba, don haka ya zama dole a sake duba lamarin.

“Don haka babu wanda ya yi magana game da wani kudi ko an biya mu ko a’a,” dan majalisar ya bayyana.
Majiyar ta ce bukatar tasu ta biyo bayan halin da ake ciki a halin yanzu na tattalin arziki bayan cire tallafin da ya janyo wahalhalu, lamarin da ya sa kayayyaki da ayyuka suka yi tashin gwauron zabi a kasar.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Sai dai dan majalisar ya ce shugaban majalisar bai yi musu alkawarin komai ba game da sake duba albashi da alawus-alawus dinsu saboda irin wannan bukata ba za a iya shigar da su cikin kasafin kudin ba ne bayan an bi tsari.
A cewar dan majalisar, shugaban majalisar ya shaidawa abokan aikinsa cewa bukatar su ba ta cikin kasafin kudin 2023.
A halin da ake ciki, domin rage tasirin cire tallafin man fetur, Majalisar Wakilai ta samu sako daga shugaban kasa Bola Tinubu a ranar 12 ga watan Yuli..
Inda wasikar ta nemi a yi masa kwaskwarima ga dokar Karin rarar kudin man fetur ta 2022.
Gyaran dai shi ne don karbar Naira Biliyan 500 domin samar da ababen more rayuwa ga ‘yan Najeriya.

Jaridar indaranka ta rawaito cewa A cikin wasikar, Tinubu ya ce bukatar ta zama dole domin baiwa gwamnati damar samar da abubuwan jin kai ga ‘yan Najeriya domin dakile illolin cire tallafin man fetur. (NAN)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending