Connect with us

News

Gwamnatin jahar Kano Na Binciken Zargin Badakalar Sama Da Billiyan 100 A Mulkin Ganduje.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano tace ta fara bincike kan zargin karkatar da wasu kudade sama da naira biliyan 100 na kananan hukumomi da tsohuwar gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta yi.

Advertisement

Hukumar ta ce ta bi diddigin yadda aka karkatar da wasu kudaden har zuwa karshe, cikin shekaru hudu.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir ya amince da nadin mutane 15 a matsayin masu ba da shawara na musamman kan fannoni daban-daban.

Shugaban Hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimingado ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar hadin gwiwa ta jihar Kano kan tafiyar da gwamnati a bude.

Advertisement

Ya koka da yadda yaki da cin hanci da rashawa ke da kalubale da yadda matsalar tayi nisa a cikin al’umma

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending