News
Gwamnatin Nijeriya Za Ta Cefanar Da Matatun Man Fetur Din Ta Ga ‘Yan Kasuwa.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kamfanin NNPC na shirin jinginar da matatun tace man Fetur na Gwamnati da suka hada da na Port-Harcourt, da na Kaduna da na Warri zuwa ga wa ‘yanda za su iya kula da su.
Indai har suka aiwatar da wannan shirin nasu to na tabbata Gwamnatin Najeriya bata shirya neman samun saukin Fetur ga talakawan Najeriya ba, sai dai neman hanyar da ita Gwamnati za ta cigaba da samun makudan kudade, fiye da yadda take samu a yanzu.
Yan Majalisa Sun Ce Daga Yanzu Zasu Dinga Sanya Batun Bunkasa Al`umma Cikin Manufofin Su
Domin gyara matatun tace mai na Gwamnati shine hanyar da Man Fetur zai iya yin sauki a Najeriya, amma barin shi a hannun ‘yan kasuwa na tabbata idan ba Allah ne ya tsare ba za’a cigaba da shan wahalar da muke ciki wadda babu ranar kawo karshen ta matukar kuma ba dawo da tallafin Man Fetur suka yi ba.
Allah ka tausaya mana, yanzu ma yaya muka kare, balle kuma mun sake shigewa hannun ‘yan kasuwa baki daya.
Idan da kowane dan Najeriya zaisan illar hakan na tabbata babu wanda zai yi farin ciki da hakan ko kadan.
