News
Tinubu Ya Gana Da Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya gana da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu da tsohon sakataren jam’iyyar Iyiola Omisore da suka sauka daga kan kujerunsu, a fadar shugaban kasa dake Villa Abuja.
Mutanen biyu sun je fadar shugaban kasar ne a tare, Kuma an gansu suna cikin annushuwa bayan kammala zaman da karfe 1 da rabi na rana, batare da sun gana da manema Labarai ba.
Abin takaici ne yadda ake samun ƙaruwar Matasa dake shaye shaye – Sarkin Kano
Sai dai rahotanni sun baiyana cewar ziyarar tasu bata rasa nasaba da rikicin cikin gida na jam’iyyar wanda yasa mutanen biyu sauka daga kan mukamansu a makon jiya.
Kazalika a ranar Litinin din makon jiya an aiyana mataimakin shugaban jam’iyyar mai kula da shiyyar Arewa Sanata Abubakar Kyari a matsayin mukaddashin shugabanta, jim kadan bayan kammala zaman kwamitin gudanarwar jam’iyyar.
