Connect with us

News

Cire Tallafi: Jihohi Uku A Arewa Sun Saka Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata, Da Dalibai

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Gwamnatocin jihohin Borno da Adamawa da Yobe sun fara daukar matakan dakile tashin gauran zabi da gwamnatin tarayya ta janyowa man fetur sakamakon cire tallafin man.

Advertisement

Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya rawaito cewa gwamnatocin jihohin da ke gudanar da kamfanonin sufurin nasu, sun ci gaba da tabbatar da cewa farashin kudinsu ya ragu fiye da yadda ake samu a wuraren hawan motoci.

Gwamnatin Najeriya Yaudarar Yan Najeriya Take Yi – NLC

A Borno Gwamna Babagana Zulum ya amince da sakin motocin bas guda 50 domin shawo kan lamarin.

Advertisement

A cewar Mallam Isa Gusau, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, motocin bas din za’a kara su ne a cikin jerin motocin sufuri mallakar jihar Borno Express Corporation.

Gusau ya ce an kuma samar da motoci 30 domin baiwa manoma musamman mazauna cikin garin Maiduguri damar tafiya kyauta zuwa wajen babban birnin jihar inda gonakinsu suke.

Advertisement

Wani dalibin Jami’ar Maiduguri, Mustapha Abdullahi, da ma’aikacin gwamnati, Ali Modu wanda suka amfana sa motocin gwamnati da ke daukar fasinja a kan Naira 50 a kowace tafiya, sun yaba wa gwamnati kan wannan matakin.

“Ina hawa motocin bas din Borno Express a kullum, ina biyan Naira 50 daga Post Office zuwa Jami’ar Maiduguri sabanin Naira 150 da motocin haya da masu tuka keke ke karba,” in ji Abdullahi.

Advertisement

A jihar Adamawa, gwamnatin jihar ta kafa kwamiti na musamman kan magance radadin cire tallafin tare da nada Dakta Amos Edgar, shugaban ma’aikata na gwamna Ahmadu Fintiri a matsayin shugaban kwamitin.

Edgar ya bayyana shirin gwamnatin Adamawa na siyan motocin bas na ma’aikata da kuma zirga-zirga a kananan hukumomi akan farashi mai sauki.

Advertisement

Ya ce sauran matakan da gwamnati ta dauka sun hada da amincewa da tallafin Naira 10,000 ga duk ma’aikata da ‘yan fansho duk wata.

Mista Labaran Salisu, Daraktan Sufuri na Ma’aikatar Sufuri ta Adamawa, ya ce za a tura wasu daga cikin motocin 250 da aka yi hayar da su a hannun ma’aikatar don ayyukan jahohi, za a tura su aikin gari a kan kudi kadan.

Advertisement

Jaridar The Nation ta rawaito cewa, A Yobe, Babban Sakataren hukumar ba da agajin gaggawa na Jihar, Dokta Mohammed Goje, ya ce ana shirin samar da sufuri kyauta ga dalibai da ma’aikatan gwamnati.

“Nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar za ta samar da motocin bas don sufuri kyauta ga ma’aikatan gwamnati da dalibai,” in ji Goje.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending