News
Gwamnatin Najeriya Yaudarar Yan Najeriya Take Yi – NLC
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wakilan kungiyar kwadagon a yammacin ranar Juma’a sun fice daga taron da kwamitin shugaban kasa kan bada tallafin da aka shirya gudanarwa a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa, da ke Abuja.
Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero ne ya jagoranci tawagar zuwa ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da misalin karfe 5 na yamma amma ba a jima ba aka hangi fitowarsu daga wurin.
Hukumar UEFA Ta Haramta Wa Juventus Shiga Gasar Zakarun Turai.
Mambobin kwamitin gudanarwar sun gana da tawagar gwamnatin a ranar Laraba, inda bangarorin biyu suka amince da sake zama ranar Juma’ar don samun takaitaccen bayani daga kananan kwamitocin gwamnati kan zirga-zirgar jama’a, albarkatu iskar gas da tura kudade.
Gwamnatin tarayya ce ta kafa kwamitin gudanarwa domin tsara shirye-shiryen shiga tsakani domin dakile radadin cire tallafin man fetur ga ‘yan Najeriya.
A hanyarsu ta fitowa daga ofishin CoS, ‘yan kwadagon sun zargi gwamnatin tarayya da amfani da tarurrukan a matsayin wata dabara ta yaudarar ‘yan Najeriya.
Wani mamban kwamitin daga kungiyar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce “Ba su shirya taron ba. Gaskiyar kenan.
“Suna amfani da hakan ne don fakewa wajen yaudarar ‘yan Najeriya. Ya kamata a samu wasu kananan kwamitoci uku na babban kwamitin zirga-zirgar, CNG da musayar kudi don yi mana bayani a cikin kwamitin gudanarwar, amma gwamnati ba ta shiryawa taron ba.”
“A cikin jawaban da suka gabatar, sun bayar da uzuri kuma sun bukaci a ci gaba da taron; taron bai samar da sakamako ba. Mu mutane ne da ke aiki bisa tsari. Don haka, idan babu shiri a cikin taro, me kuke yi? Za ku dage sauraron karar saboda rashin tsari.
“Babu wanda zai sadu da su. Shugaban ma’aikatan ba ya nan; suna daukar mu kamar yara.”
Wasu rahotanni sun ce shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila ya jira tawagar kwadagon tare da sauran ‘yan tawagar.
Amma tawagar ƙwadago da suka shirya daga NLC da ƴan kwadago sun ɗan samu ɗan jinkiri yayin shigarsu fadar gwamnatin kan batutuwan share fage. Dalilin jinkirin da aka samu shi ns, ba a aike da sunayen mambobin tawagar zuwa bakin kofa da wuri ba domin tantancewa.
Daga baya Gbajabiamila ya ba da uzurin halartar wurin saboda al’amuran da ke cikin fadar ta Villa, yayin da sauran ‘yan tawagar gwamnati ke jiran isowar tawagar kwadago.
“An tsare mu a kofar gidan gwamnatin,” daya daga cikin shugabannin tawagar ‘yan kwadago ya shaida wa manema labarai.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Taron na ranar Juma’a zai kasance karo na hudu a jerin tarurrukan da Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago suka yi tun bayan cire tallafin man fetur.
