News
An Tabbatar Da Barkewar Cutar Anthrax Akan Dabbobi 6 A Legas
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Gwamnatin jihar Legas ta ce an tabbatar da cewa dabbobi shida a jihar suna dauke da cutar anthrax.
Ma’aikatar noma ta jihar ta bakin babban sakatarenta, Olatokunbo Emokpae, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, inda ya ce an gano cutar a tsibirin Legas da Agege.
Shugaba Tinubu Ya Bada Kwangilar Bincike Akan babban bankin kasa CBN
Emokpae ya ce an kwace dabbobin an kona su tare da binne su, don hana yaduwar cutar, ya kara da cewa ba a samu rahoton kamuwa da cutar a jikin dan adam ba tun bayan da aka samu cutar a jihar.
Anthrax kamuwa da cuta ce mai yaduwa amma Yawanci tana shafar dabbobin kamar shanu da tumaki, da kuma awaki.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
