News
Shugaba Tinubu Ya Bada Kwangilar Bincike Akan babban bankin kasa CBN
DAGA KABIRU BASIRU FRULATAN.
Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya nada wani mai bincike na musamman Jim Osayande da zai binciki babban bankin kasa CBN da ayyukan da suka shafi gudanarwar bankin.
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban kasar kuma aka aikawa Obazee, babban jami’in hukumar bayar da rahoto kan harkokin kudi ta Najeriya.
Shugaban Chadi Ya Gana Da Jagoran Sojojin Da Suka Yi Juyin Mulki a Nijar
Tinubu ya kuma aikewa Obazee kwafin umarninsa na dakatar da Godwin Emefiele amatsayin gwamnan babban bankin.
Wannan ci gaban na zuwa ne a daidai lokacin da Emefiele ke fuskantar shari’a.
Yayin da Emefiele ke ci gaba da kasancewa a tsare a hannun DSS a makon da ya gabata wata kotu ta bayar da belinsa amma hukumar ta sake kama shi nan take.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
