News
Tinubu Yace Za Su Kara Mafi Karancin Albashin Ma’aikata
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na duba yiwuwar kara mafi karancin albashin ma’aikata.
Tinubu ya fadi haka ne a jawabin da ya yi wa ’yan kasa a Yammacin wannan Litinin din.
“Karin albashi na nan tafe,” a cewarsa.
“Da zarar mun daddale game da mafi karancin albashi da kuma sauran abubuwa, za mu saka shi cikin kasafin kudi domin fara aiki cikin gaggawa.
“Tuni mun kaddamar da tsarin sake duba albashin ma’aikata.”
Haka kuma a jawabin nasa, Tinubu ya ce gwamnatinsa ta dauki tsauraran matakai ne saboda sun zama dole, “kuma babu waɗanda suka fi su sauki.”
“Da a ce akwai hanyoyin da suka fi su sauki da na bi,” in ji shi.
“Abin da zan iya yi kawai shi ne daukar matakan da za su saukaka yanayin.
“Gwamnatina za ta tabbatar da yin aiki tare da dukkan jihohi don rage radadin da ’yan kasa ke ji.”
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
