News
Kananan Hukumomi 171 A Jihohi 14 Na Cikin Hadarin Kamuwa Da Cutar Mashako
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa kimanin kananan hukumomi 171 a jihohi 14 na cikin hadarin kamuwa da cutar Mashako.
Ta ce yankunan da abin ya shafa sun hada da: dukkanin kananan hukumomin dake jihohin Kano, Katsina, Babban Birnin Tarayya, Yobe, Kaduna da Bauchi.
Nasir El-Rufai na cikin mutum uku da ba a tabbatar wa mukaman minista ba
Kananan hukumomi guda 20 da ke jihohin (Gombe, Jigawa, Borno, Nasarawa, Plateau da Zamfara da kuma kananan hukumomi bakwai a jihohin Legas da Osun na cikin wadanda zasu fuskanci wannan cutar..
Hakan ya zo ne a daidai lokacin da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta kasa, da Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya da kuma abokan hadin gwiwa, ke tattara kayan aiki domin tunkarar barkewar cutar a jihohin.
Babban Sakatare a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya Olufunsho Adebiyi, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja jiya, ya ce bayanan da suka samu, sun nuna yadda cutar Mashakon ta bulla a kananan hukumomi 25 da ke Bauchi, Katsina, Yobe da kuma Kaduna wanda yanzu suke a mataki na farko. A cewarsa, jihohi 14 na matakin na biyu, wadanda suka hada da: Katsina, Kaduna, Kano, Yobe, FCT, Bauchi, Gombe, Jigawa, Borno, Nasarawa, Plateau, Zamfara, Lagos da Osun.
