News
SUDAN:Yara sama da miliyan 14 ke buƙatar agaji a Sudan
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.
Hukumomin agaji na ƙasa da ƙasa sun yi gargadin cewa, watanni hudu da aka kwashe ana rikici a kassar Sudan, lamarin na ƙara ƙamari, tare da tilasta mutane da dama yin hijira daga matsugunansu.
Bbc Hausa ta rawaito cewa Lamarin na faruwa ne yayin da miliyoyin mutane ke gab da faɗawa cikin yunwa a kasar.
Hukumar Kwastam Sun Kwace Harsashi Guda 1,245 Da Aka Yi Fasa Kwaurin Su A Buhunan Shinkafa
Cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, shugabannin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa suka futar sun ce yara miliyan 14 na buƙatar agajin gaggawa, yayin da sama da mutane miliyan huɗu sukayi hijira daga gidajensu.
Sun yi kira ga ɓangarorin da ke rikici da juna da su kawo ƙarshen faɗan tare da tabbatar da samun damar kai kayan agaji cikin aminci.
Wakilin BBC ya ce hukumomin agajin sun yi gargaɗin cewa lokaci na ƙure wa manoman ƙasar wajen shuka amfanin gona.
Sun kuma ce za su ci gaba da ƙoƙarin ganin an kai agaji duk inda ya dace.
Yankin Darfur da kuma babban birnin kasar, Khartoum, na fama da tashe-tashen hankali tsakanin sojojin Sudan da kuma dakarun RSF.
