News
Mutane 5 sun mutu a hatsarin mota a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja
![](https://indaranka.com/wp-content/uploads/2023/08/images-5-2.jpeg)
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Wani hatsari da ya afku a hanyar Kaduna zuwa Abuja a yau Talatar ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar, yayin da wasu fasinjoji shida suka samu munanan raunuka.
A cewar Mallam Ahmed Jibril, wani ganau wanda kuma fasinja ne a daya daga cikin motocin da suka yi karo da juna, hatsarin ya faru ne sakamakon wuce gona da iri da direbobin motar keyi.
Sai Da Ya Samu Izinin Shugabannin PDP Kafin Ya Karbi Matsayin Minista–Wike
Jibril, wanda ya samu dan Karmin rauni, ya ce suna tafiya ne a cikin wata motar bas mai mutane 18 daga Abuja zuwa Kano, sai motarsu ta yi karo da wata motar Toyota pickup da wani direba daya tilo daga Kaduna, kusa da Kateri.
An kwashe gawarwakin fasinjojin da suka mutu da wadanda suka jikkata zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba, kamar yadda ya shaidawa jaridar DAILY POST.