News
Wasu matasa sun kashe wani Tsoho mai shekaru 50 da ake zargin da satar Shanu a Jigawa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wasu fusatattun matasa sun kashe wani Tsoho mai shekaru 50 da ake zargin da satar Shanu mai suna Yahaya Adamu a karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa.
Wani mazaunin garin ya shaidawa jaridara DAILY POST cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata inda gungun barayin shanu suka afkawa kauyen Unguwan Toro inda suka yi awon gaba da dabbobinsu.
Mutane 5 sun mutu a hatsarin mota a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja
Ya ce a dalilin haka ne wasu gungun matasa suka taru tare da bin diddigin sawun barayin, inda daga bisani suka kai farmaki kan wadanda ake zargin da hannun sa a satar .
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarsa, “’Yan sanda a ranar 16 ga Agusta, 2023, da misalin karfe 11:00. An samu rahoton cewa, barayin dabbobi sun kai farmaki gidan wani Hardo Musa mai shekaru 60 a kauyen Unguwar Toro karamar hukumar Babura, inda suka yi awon gaba da tunkiyarsa da ba a tantance adadinsu ba.
Shiisu ya ce da samun labarin, ‘yan sandan da ke aiki da sashen Babura, sun yi gaggawar zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka kai wanda abin ya shafa babban asibitin Babura domin yi masa magani.
Ya ce wanda ake zargin ya rasu ne a ranar Litinin yayin da yake karbar magani.
Kakakin ‘yan sandan ya ce wasu mutum uku da ake zargi.
An kama Kabiru Muazu, Hardo Musa, da Saidu Wanzam bisa laifin aikata laifin.
Ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike.