News
Gwamnatin Jahar Kano Zata Kafa Kwamitin Nemarwa Daliban Kano Guraben Karatu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Gwamnatin jihar Kano na wani yunkuri na kafa kwamitin nemowa ‘yan jihar Kano Guraben karatu, domin tabbatar da cewar ‘yan asalin jihar kano, sun rika cin gajiyar guraben karatun da ake ware masu a manyan makarantun kasar nan.
Kwamishinan Ilimi na makarantu masu zurfi na jihar Kano,Dr.Yusuf Ibrahim Kofar mata ne ya baiyana haka a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka shirya a kwalejin share fagen shiga jami’a dake nan Kano.
Wasu matasa sun kashe wani Tsoho mai shekaru 50 da ake zargin da satar Shanu a Jigawa
Sanarwar da kakakin ma’aikatar Sunusi A kofar Naisa ya fitar, ta Ambato kwamishinan na cewar matakin zai rage yawan dogara da manyan makarantun da ake dasu a jihar Kano, wajen samun guraben karatu.