News
An Dawo Da Shirin Bautar Kasa A Borno Bayan Shekara 13
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumar kula da shirin masu hidimtawa kasa ta fara aikin wayar da kan masu hidimitawa kasa kafin rarraba su zuwa wurare daban daban a karon farko, bayan shafe shekara 13 batare da gudanar da shirin ba, tun bayan da aka dakatar da shi a shekarar 2011, saboda matsaloli na rashin tsaro.
Jami’in kula da shirin a jihar, Mohammed Adamu a lokacin da yake jawabi yayin bukin rantsar da rukunin masu hidimtawa kasar a ranar Talata, ya jinjinawa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum saboda namijin kokarinsa wajen ganin an ci gaba da shirin a jihar.
Gwamnatin Jahar Kano Zata Kafa Kwamitin Nemarwa Daliban Kano Guraben Karatu
An yiwa masu bautawa kasar sansani a kwalejin horas da malaman larabci dake jihar, wadda ke zama matsagunnin wucin gadi , a yayin da hadakar jami’an tsaro suka tsaurara tsaro a wajen.
Shima a nasa jawabin gwamna Zulum, ya baiyana farin cikinsa wajen ganin dawowar shirin, inda ya ce yunkurin ya sake tabbatar da dawowar zaman lafiya da tsaro a jihar bayan shafe shekaru da dama tana fama da matsalar mayakan tada kayar baya.