Connect with us

News

Kungiyar AROGMA sun hada hannu da kamfanin NNPCL da masu zuba jari na kasashen waje don Samar da makamashi

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Yan kasuwar Arewa masu sana’ar man Fetur da iskar gas sun hada hannu da kamfanin NNPCL da masu zuba jari na kasashen waje wajan Samar da man Fetur da kuma iskar gas a yankin arewacin najeriya.

Kungiyar na shirin ganin canjin makamashi da sauran makamashi kamar su Premium Motor Spirit, PMS, wanda aka fi sani da petroleum da kuma Compressed Natural Gas, CNG, a daidai lokacin da kungiyar dillalan mai da iskar Gas ta Arewa, AROGMA, ke shirin gayyato kamfanonin kasashen waje.

Advertisement

Ministan Shugaba Tinubu Ya Sanar da Ranar da Matatar Mai Ta Fatakwal Za ta Fara Aiki

Zababben shugaban kungiyar Bashir Ahmad Dan-Mallam ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Kano ranar Juma’a.

A cewar Dan-Mallam, Kungiyar, tare da hadin gwiwar Kamfanin Mai na Kasa NNPCL na shirin gayyato kamfanoni daga Qatar, Turkiyya, Jamus da kuma Indiya domin samar da iskar gas a Najeriya.

Advertisement

Ya bayyana cewa tuni kungiyar ta tuntuɓi abokan hulɗar su na waje kuma sun kan nazarin da kuma shawarwarin kan lamarin.

Shugaban ya yi nuni da cewa, aikin zai zama babban nasara ga Nijeriya, kuma zai zama wani muhimmin ci gaban kasar nan musamman a yankin Arewa.

Advertisement

Ya kuma kara da cewa hakan zai saukaka Matsalar tattalin arzikin da kasar ke fama da shi, musamman a Arewacin Najeriya, sakamakon cire tallafin man fetur.

Dan-Mallam ya kuma yabawa kokarin da mahukuntan na NNPCPL suke yi bisa goyon baya da jajircewa da suke bawa ’yan kasuwa wajen saka hannun jari a wasu tsare-tsare na canza man fetur, amfani da CNG da canza sheka, Autogas, da kuma matatun mai da dai sauransu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending