News
Yawan karanta alqur ani mai girma da yawaita istightlfari ne kadai zai cire alumma daga kuncin Rayuwa.
DAGA SAMEER IDIRS HOTORO
Wani malamin addinin musulunci dake unguwar Hotoro Dogon-Rimi a karamar hukumar nasarawa, alaramma Sani Bashir Hotoro yace, Yawan karanta alqur ani mai girma da yawaita istightlfari ne kadai zai cire alumma daga kuncin Rayuwa.
Bayanin hakan na zuwa ne yayin Bakin saukar karatun alqur’ani mai girma da makarantar Nasara Nurul-Huda Al-Islamiyya ta gudanar da safiyar yau a unguwar Hotoro Dogon-Rimi dake karamar hukumar Nassarawa.
Bakin saukar karatun alqur’ani mai girma Karo ba Hudu Na dalibai Talatin Da Uku 33 da Mahaddata Biyu 2 tare da dalibai 17 masu Walimar Izu Arba’in.
Alaramma Sani ya kuma ja hankalin iyayen yara dasu ke sanya idanu akan karatun ‘ya’yansu domin samun ingantaccen ilimin addini dama na zamani baki daya.
Wakilin Jaridar Indaranka Sameer Idris Hotoroya ruwaito cewa taron ya samu halartar manyan baki ciki harda sardaunan kano Malam Ibrahim shekarau
