News
Gwamnatin Jahar Kano Ta Sauke Shugaban Asibitin Hasiya Bayero
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta sauke shugaban asibitin yara na Hasiya Bayero bisa zargin rashin iya shugabanci.
Wata sanarwa dauke da sahannun jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Samira Suleiman, ta ce an dauki matakin ne bayan doguwar tattaunawa da kwamishinan lafiya Dr. Abubakar Yusuf Labaran da shugaban hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano, Dr. Mansur Mudi Nagoda.
Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.
Sanarwar ta zargi shugaban asibitin na Hasiya Bayero da aka sauke da gazawa wajen tsara ma’aikata tare da aiwatar da manufofin gwamnati da aka ayyana na duba marasa lafiya da kuma kula da su kyauta.
Sanarwar ta kuma ruwaito Dr. Nagoda na korafin cewa shugaban ya gaza sarrafa ma’aikatansa domin samar da kulawa yadda ya kamata.
An sanar da Dr. Ibrahim Ibn Muhammad amatsayin sabon shugaban asibitin na Hasiya Bayero.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
