News
Gwamnan jihar Kano Alh Abba Kabir Yusuf ya yi alhinin rasuwar Barista Halliru Danga Maigari
DAGA MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnan jihar Kano Alh Abba Kabir Yusuf ya yi alhinin rasuwar Barista Halliru Danga Maigari wanda ya taba zama shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano wanda ya rasu da yammacin yau bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin jiga-jigan shari’a kuma shugaban al’umma wanda ya bayar da gudunmawa sosai wajen ci gaban al’ummarsa da karamar hukumarsa da kuma jihar Kano.
Korar da kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Kano ta yi, ta bawa ‘yan Najeriya da dama mamaki.
A cewar Gwamnan, “cikin zuciya cike da alhini amma muna biyayya ga ikon Allah ne muka samu labarin rasuwar Barista Halliru Danga Maigari bayan doguwar jinya.
Amadadin gwamnati da na al’ummar jihar nan muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalansa, al’ummar RiminGado, jihar Kano da fatan Allah SWT ya jikansa da rahama, kuma Jannatul Firdausi ta kasance makomar sa
Marigayi Barista Halliru Danga Maigari ya kasance mai goyon bayan jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) wanda masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a mazabarsa (RiminGado) da ma wajensa suka yaba da gudummawar da ya bayar.
wani labarin kumaKorar da kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Kano ta yi, ta bawa ‘yan Najeriya da dama mamaki.
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro