News
Kungiyoyin NLC Da TUC Na Hada Kan Ma’aikata Don Tafka Gagarumin Yajin Aiki
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyoyin Kwadago da suka hada da kungiyar kwadago ta Njeriya NLC da Kungiyar ‘Yan Kasuwa (TUC) sun kammala gangamin hada kan mambobinsu da kungiyoyinsu domin shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin kasar nan daga ranar Talata 3 ga watan Oktoba, 2023.
Lamarin ya biyo bayan kauracewa taron da gwamnatin tarayya ta shirya a ranar Juma’a a matsayin mataki na karshe na dakile yajin aikin.
Kotun Daukaka Kara Ta Samu Korafe-korafen Zabubbukan na 2023 Guda 1,209
Tuni dai kungiyoyin kwadagon suka tsaya tsayin daka na cewa babu ja da baya kan shirin yajin aikin.
Ƙungiyoyin guda biyu, wadanda suka sanar da fara yajin aikin bayan wani taron manema labarai na hadin gwiwa a ranar Talata a Abuja, sun ce yajin aikin ya biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya wajen magance wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur da sauran munanan manufofin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Sun kuma zargi gwamnatin kasar na. da kin shiga tattaunawa da su duk da wa’adin kwanaki 21 da yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da suka yi a ranakun 5 da 6 ga watan Satumba.
Wani labarin kuma Kotun Daukaka Kara Ta Samu Korafe-korafen Zabubbukan na 2023 Guda 1,209
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro