Connect with us

Business

Yanzu-Yanzu: Kamfanin BUA ya rage farashin kuɗin Simintin sa

Published

on

Abdussamad Isyaka Rabi’u

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

 

Hukumar gudanarwar kamfanin siminti na BUA ya sanar da rage farashin kudin simintin zuwa Naira 3,500 daga ranar 2 ga watan October na shekara ta 2023.

Indaranka ta rawaito hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar gudanarwar kamfanin ta sanyawa hannu .

Sanarwar tace kamfanin ya ɗauki wannan matakin ne domin saukakawa al’ummar Nigeria, a kokarin kamfanin na saukakawa abokan huldar su .

Advertisement

Idan za’a iya tunawa Indaranka ta rawaito Shugaban kamfanin Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi’u ya ce zasu ɗauki wannan mataki domin saukakawa al’ummar Nigeria saboda halin da ake ciki.

A lokacin da ya ziyarci Shugaban kasa Tinubu domin sanar da shi shirin da suke na wannan mataki, wanda kuma ga shi yanzu ya tabbata.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending