News
An Kama Barayin Jaririya Don Tsafi A Jahar Kano

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kotun Shariar Musulunci da ke zamanta a Gama PRP a Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare wasu mutane biyar a gidan yari kan yunkurin satar wata jaririya ’yar kwanaki takwas da haihuwa domin yin tsafi da ita.
Mai gabatar da kara Aliyul Abidin ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhuma sun hada baki domin sace jaririyar wacce ake zargin tsafi za a yi tsafi da ita, su kuma za a biya su Naira miliyan 30 a matsayin ladan aikinsu.
Kungiyoyin kwadago suna duba yiwuwar janye batun tafiya yajin aiki bayan ganawa da gwamnatin tarayya
Jaridar Aminiya ta rawaito cewa Sai dai maza biyu daga cikin wadanda ake zargi sun musanta laifukan, a yayin da sauran ukun da ake zargi kuma suka amsa laifin.
Alkalin kotun Mai sharia Nura Yusuf Ahmad ya bayar da umarnin tsare dukkansu, maza hudu da mace daya a gidan gyaran hali tare da dage shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Oktoba, 2023.
Wani labarin kuma Gwamnatin Jihar Kano Zata Fara Bai Wa ‘Yan Mata 45,000 Tallafin N20, 000
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro