News
Rundunar Yan Sanda Sun Kama Mawaƙi Naira Marley Kan Mutuwar Mohbad
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Rundunar ƴan sanda a jihar Legas ta ce tana tsare da tauraron waƙoƙin Afrobeats, Naira Marley kan mutuwar tsohon abokin aikinsa Mobhad.
Mai magana da yawun rudunar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana haka da yammacin Talata.
Ƴan sanda sun kama iyayen da suka yi wa yaransu auren wuri a kasar Indiya
Ya ce ”An tsare Azeez Fashola wanda aka fi sani da Naira Marley domin yi masa tambayoyi da sauran ayyukan bincike.”
Tun bayan mutuwar Mobhad a watan Satumba, ƴan Najeriya musamman matasa ke zargin Naira Marley da hannu a lamarin sanadiyyar saɓanin da suka samu kafin raba-gari.
Sai dai Naira Marley ya sha musanta zargin.
Matasa da dama sun gudanar da zanga-zanga a manyan biranen kasar domin neman hukumomi su gudanar da bincike kan lamarin.
Hakan ya sa rundunar ƴan sanda ta zakulo gawar Mobhad da niyyar gudanar da bincike don neman gano sanadiyar mutuwar sa.
Wani labarin kuma Ƴan sanda sun kama iyayen da suka yi wa yaransu auren wuri a kasar Indiya
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro
