News
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ayyana Laraba 4 ga Oktoba, A Matsayin Hutu
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ayyana Laraba 4 ga Oktoba, 2023 a matsayin ranar hutu domin tunawa da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Kwamishinan ma’aikatar yada labarai da harkokin cikin gida ta jihar, Baba Halilu Dantiye, MON,ne ya bayyana hakan ga kungiyoyin yada labarai na jihar.
Rundunar Yan Sanda Sun Kama Mawaƙi Naira Marley Kan Mutuwar Mohbad
Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da lokutan bukukuwa domin yin tunani a kan koyarwar Manzon Allah
Ya kuma bukaci jama’a da su rika yin addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaba a Kano dama Najeriya baki daya.
Ya kuma roki Allah da ya ganar damu wannan lokaci mai wahala, ya kuma bamu albarkar damina a wannan damina da kuma lokacin noman rani mai zuwa.
Wani labarin kuma Rundunar sojin za ta yi bincike a kan zargin rashin ciyar da dakarunta da ke filin daga
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro
