Connect with us

News

Gwamnatin Tarraya Na Barazanar Daina Biyan Albashi Ga Ma’aikatan Da Suka Bijirewa Rijista Da IPPIS

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar daina biyan albashin duk wani Ma’aikacin gwamnati da bayanansa basa cikin tsarin tantace bayanan biyan albashi na Bai daya IPPIS daga ranar juma’a mai zuwa 27 ga watan da muke ciki.

Shugabar ma’aikata ta Kasa, Dr Folasade Yemi-Esan ce ta bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da Daraktan yada labaranta Mohammed Ahmed ya fitar.

Yau Alhamis Kotun Koli A Zata Yanke Hukunci Kan Shari’ar Zaben Shugaban Kasa Na 2023

A cewar sanarwar, An fara aikin tantancewar ne ta tsawon mako biyu, wadda za ta kare a ranar Juma’a, domin inganta hanyoyin biyan albashi ga ma’aikata.

Ta yi gargadin cewa ba za a kara biyan duk wani albashi ga ma’aikacin gwamnati da bayanansa basa cikin tsarin.

Advertisement

A wani labarin kuma Yau Alhamis Kotun Koli A Zata Yanke Hukunci Kan Shari’ar Zaben Shugaban Kasa Na 2023

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending