Business
Kamfanin Dangote ya zargi BUA da daukar nauyin yada labaran karya akansa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Katafaren Kamfanin Dangote da ke Najeriya ya musanta zargin cewar ya sanya kansa cikin haramcaciyar musayar kudaden waje, inda ya gargadi masu yada irin wannan zargin cewar ya na yiwa kasa zagon kasa, da su kaucewa yin haka.
Kamfanin ya gabatar da wannan gargadi ne sakamakon wasu rahotannin da aka wallafa a kafofin intanet dake zargin cewar shugaban kwamiti na musamman da shugaban Najeriya ya kafa Jim Obazee domin binciken ayyukan Babban Bankin Najeriya a karkashin jagorancin Godwin Emefiele na gudanar da bincike a kan sa saboda hannu wajen wannan badakalar da kuma halarta kudaden harum.
Ku Guji Manyan Otal A Najeriya, Amurka Ta Gargadi ‘Yan Kasarta
Sanarwar da kamfanin ya gabatar ta ce, Dangote ya bayyana rahotanin a matsayin masu tsauri, yayin da ya zargi abokin adawarsa, wato kamfanin BUA da hannu a ciki dumu dumu.
Dangote yace tun daga shekarar 2016 aka fara yada irin wadannan labarai na kanzon kurege a jaridun BusinessDay da Leadership, inda yace sun sake farfado da su ne yanzu domin gabatar da su kamar wasu sabbin labarai.
Kamfanin yace abin takaici ne yadda a ranar 14 ga watan Maris na shekarar 2016, Jaridun BusinessDay da Leadership suka wallafa rahotan cewar Kamfanin Dangote ya karkata Dala biliyan 3 na kudaden waje zuwa wasu kamfanoninsa dake wajen Najeriya, matakin dake da nasaba da halarta kudaden haramun.
Dangote ya ce wancan rahotan da aka yi a shekarar 2016 shine kuma aka sake wallafa shi a yanzu da sunan wani Ahmed Fahad, a matsayin korafin da aka gabatarwa shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma Jim Obazee, shugaban kwamitin bincike na musamman dake gudanar da bincike a kan ayyukan Babban Bankin Najeriya.
Kamfanin ya ce abin takaici shine yadda wasu kafofin intanet suka dinga daukar labarin suna wallafa shi da zummar bata masa suna.
Dangote ya ce yunkurin wadanda suka kitsa wannan labari na kawar da hankalin jama’a da kuma farfado da tsohon labarin abin takaici ne, ganin yadda wadancan jaridu guda 2 da suka wallafa shi a shekarar 2016 suka fito fili suka kuma nemi gafarar shugabannin kamfanin Dangoten da kuma janye labaran da suka yi a kai baki daya.
Kamfanin ya ce Jaridun BusinessDay da Leadership sun tabbatar da cewar kamfanin BUA ne ya dauki nauyin wallafa rahotanin.
Dangote yace yana samo kudaden waje domin gudanar da ayyukan sa ne ta hanyoyin bankuna kamar yadda dokokin CBN suka tanada, kuma suna gabatar da takardun da suka dace wajen samun kudaden sayen kayayyakin aiki da kuma kafa kamfanonin su ciki harda na siminti.
Kamfanin ya ce an kuma bayyana karara yadda aka gudanar da hada hadar kudaden da kuma lokacin da za’a biya basussukan da aka karba kamar yadda ka’idodin duniya suka tanada.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
