Connect with us

Business

Zamu  Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Takardun Kudi Na Naira  – CBN

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Babban Bankin kasa CBN na gargadin kin amincewa da duk wata takardar kudi ta banki saboda fargabar cewa tsofaffin takardun kudi na iya daina shiga kasuwa nan da watan gobe na Disambar 2023.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba mai dauke da sa hannun mai magana da yawun bankin, Isah Abdulmunin, Babban Bankin kasa CBN ya ce bai bayar da umarnin daina amfanin da tsoffin takardun kudin na Naira ba.

Advertisement

Zaben Bayelsa:Ba Za Mu Kidaya Kuri’un Wuraren Da Aka Samu Tashin Hankali Ba – Hukumar INEC

Sanarwar ta kara da cewa, an umarci dukkanin rassan Babban Bankin kasa CBN da su ci gaba da fitar da tsofaffin takardun kudi a adadi mai yawa ga bankuna don ci gaba da zagayawa.

Idan ba a manta ba a watan Maris ne kotun koli ta bayar da umarnin ci gaba da aiki da tsofaffin takardun kudi na Naira 200 da 500 da kuma Naira dubu 1 har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, bayan da jihohi 16 suka shigar da kara domin kalubalantar sahihancin bullo da sabuwar manufar chanjin takardar kudi.

Advertisement

A wani labarin kuma Zaben Bayelsa:Ba Za Mu Kidaya Kuri’un Wuraren Da Aka Samu Tashin Hankali Ba – Hukumar INEC

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending