Entertainment
Hukumar Hisbah Na Tayin Aurar Da ‘Yan TikTok A Jahr Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta yi alkawarin shiryawa da kuma daukar nauyin Aurar da matasa Maza da Mata ‘yan TikTok a wani mataki na kawar da rashin ‘Da’a a cikin al’umma da kyautata zamantakewa.
Babban Kwamandan hukumar Sheik Aminu Ibrahim Daurawa ne ya yi wannan alkawari lokacin da ya yake fadakar da ‘yan TikTok da suka amsa gayyatar hukumar a ranar litinin.
Kungiyoyin Kwadago Za Su Tsunduma Yajin Aiki A Ranar 14 Ga Nuwamba
Ya ce hukumar ta damu akan yadda wasu matasan Maza da Mata suka mayar da TikTok ƙafar cin mutunci da rashin tarbiya Wanda hakan ke zubar da kimar Kano.
Koda ya ke Sheik Daurawa ya yabawa wasu masu gudanar da Sana’oi da kasuwanci da masu koyar da hikimomin zamantakewa ko Ilimin Addini da na zamani a TikTok, ya ce hukumar a shirye ta ke Aurar da matasan na TikTok Maza da Mata da suke son yin Aure, Inda ya bukaci su zama jakadu na gari.
A wani labarin kuma Kungiyoyin Kwadago Za Su Tsunduma Yajin Aiki A Ranar 14 Ga Nuwamba
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.