Connect with us

News

An haramta taruka da daddare a jihar Katsina

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Gwamnatin jihar katsina tace ta haramta yin kowane irin taro da daddare ko da kuwa na addini ne muddin ba sallolin da suke farillai ba.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da al’adu da harkokin cikin gida Bala Salisu Zango ya fitar, tace dole ne kuma daga yanzu duk wani taro da za a yi ko da rana wajibi ne a nemi sahalewar baturen ‘yan sandan yanki wato DPO

Duk Wadanda Muke Bi Bashi Sai Sun Biya —Kamfanin MTN

Sanarwar ta kara da neman hadin kan al’umma akan wannan doka da ta ce an dauka ne domin kare dukiya da rayukan al’ummar jihar

A wani labarin kuma Duk Wadanda Muke Bi Bashi Sai Sun Biya —Kamfanin MTN

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

 

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending