Connect with us

News

Babbar Magana: An Kame Dan Takarar Gwamna A Jahar Kogi 

Published

on

Olayinka Braimoh

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

An cafke dan takarar gwamna na jam’iyyar AA a zaben gwamna da ke gudana a jihar Kogi, Olayinka Braimoh

Kame dan takarar gwamnan ya biyo bayan samun wasu muhimman kayayyaki a wajen sa

Dino Melaye Ya Bukaci INEC Ta Soke Zaben Kananan Hukumomi Biyar

Tuni magoya bayan dan takarar suka shiga cikin rudani biyo bayan kamen

An kama dan takarar gwamna na jam’iyyar Action Alliance AA a zaben gwamna da ke gudana a jihar Kogi, Olayinka Braimoh.

Advertisement

Mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Musa Yakubu, wanda ya tabbatar wa manema labarai kamun ya ce jami’an tsaro sun kama shugaban nasa a Kabba.

Musa ya bayyana cewa an kama dan takarar da kuma bakwai daga cikin bayanan tsaronsa bayan an gano kayan yakin neman zabe a cikin motarsa

DAILY POST ta rawaito cewa ba ta samu damar jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar kan batun ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Tun da farko mai taimaka wa Braimoh kan harkokin yada labarai ya tayar da husuma kan inda dan takarar AA yake.

“A karshe da na ji ta bakinsa shi ne da safe lokacin da ya kira shi daga garin Kabba, amma duk kokarin da aka yi na samun shi tun daga wancan lokacin ya ci tura,” in ji Yakubu.

“An kashe layukan wayarsa, gami da tawagarsa.”

Advertisement

A wani labarin kuma Dino Melaye Ya Bukaci INEC Ta Soke Zaben Kananan Hukumomi Biyar

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending