News
KNSG ta shirya taron karawa juna sani na kwanaki biyu na masu ruwa da tsaki KSCHMA DRF, na asibitoci.
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
A yunkurinta na karfafa da kuma daidaita ayyukan shirin samar da magunguna cikin rahusa (DRF) a jihar Kano, Gwamnatin Jihar Kano, ta karkashin Kwamitin Samar da Kayayyakin Kiwon Lafiya mai Dorewa na Jiha (SHCSS) ta shirya taron karawa juna sani na kwanaki biyu na masu ruwa da tsaki don fitar da tsarin da za hade DRF na Hukumar Taimakekeniyar Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA) da kuma DRF na asibitoci.
Mahalarta taron sun fito ne daga ma’aikatar lafiya da hukumominta da suka hada da Darakta Janar Hukumar Samar da Magunguna (DMCSA), Darakta Janar na Hukumar Kula da Cibiyoyin Kiwon Lafiya Masu Zaman Kansu (PHIMA), Sakataren Zartarwa na Hukumar Taimakekeniyar Lafiya (KSCHMA) da kuma Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Manyan Asibitoci da daraktocin da suka dace.
Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi ta Duniya Ta Kira Taron Gaggawa Kan Yakin Falasdinawa
Hakan na kunshe ne cikin wata Sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Ma’aikatar Lafiya Ibrahim Abdullahi ya turawa Jaridar Inda Ranka.
Haka kuma Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa makasudin taron shi ne wayar da kan mahalarta su fahimci manufar tsarin samar da kayayyakin kiwon lafiya mai dorewa a jihar Kano, da yin amfani da DRF don samar da kayayyakin kiwon lafiya ba tare da katsewa ba ga abokan huldar KSCHMA, da fahimtar alakar da ke tsakanin DRF da sauran shirye-shirye da ayyukan sassan da ke cikin asibitoci da kuma fahimtar fa’idar haɗe DRF tare da wasu shirye-shirye kamar KSCHMA, NHIS, BHCPF, da sauransu waɗanda su ma ke samar da magunguna.
Bayan gabatar da makaloli, tattaunawa da amfanar da juna wasu ilmonmin da aka sani, mahalarta sun lura cewa akwai rauni wajen bibiya a tsarin DRF da ita kanta KSCHMA, da kuma yawaitar yankewar magunguna a asibitoci da ke sanya abokan huldar KSCHMA su kasa samun magungunan da aka rubuta musu.
Har ila yau, sun kuma lura cewa DMCSA tana fama da ƙalubalen kuɗi, sannan kayan aikin da take da su ba su isa ba suna buƙatar haɓaka kari kan buƙatar da ake da ita ga DMCSA ta samo ƙarin jari da kuma inganta ƙwarewar ma’aikatanta.
Har ila yau, sun lura cewa wasu asibitoci, musamman cibiyoyin lafiya matakin farko, suna buƙatar shirye-shiryen samun jarin gaggawa don shigar da su cikin shirin, da kuma sayen magunguna da asibitoci kan yi ba a DMCSA ba.
A karshen taron, mahalartan sun amince da manufar hade KSCHMA DRF da DRF na asibitoci da kuma inganta tsarin hadewar, wanda zai hada da sayen magunguna, ajiyewa, da kuma iya alkintawa.
Har ila yau, sun amince da shigo da asibitoci masu zaman kansu a wajen sayen magunguna da sauran kayayyaki a DMCSA tare da sake mayar da dukkan masu ruwa da tsaki game da sabon tsarin hadewar don aiwatar da su cikin sauƙi ga masu bibiya, manajoji da masu aiwatar da shirin a matakin asibitoci, da za a yi a lokuta daban-daban.
Haka kuma, sun amince cewa a samar da ihisani ga ma’aikatan da suke aiki tukuru, yayin da za a hukunta wadanda suka karya doka a kowane mataki, kari kan kulla alaka tsakanin DMCSA da sauran hukumomi a bangaren lafiya.
Bugu da kari, sun amince da kafa kwamitin kar-ta-kwana da zai tabbatar da bin tsarin da aka kafa; shigo asibitoci cikin tsarin ya kasance mataki-mataki, farawa da asibitocin da aka zaba a matsayin gwaji; lallai a rinka sanya ido da bibiya sosai ga asibitocin da za a gwada tsarin gudanar don sanin nasara ko akasin haka na haɗe DRF da kuma rashin amincewa da yin sayayya kai a wajen DMCSA.
Taron ya kasance mai jan hankali sosai kuma mahalarta sun ba da gudummawa sosai wajen samar da tsarin haɗa KSCHMA DRF da DRF na asibitoci, tare da babbar gudummawa daga KSCHMA da DMCSA.
Darussa masu amfani da aka samu a yayin bitar sun samu ne sakamakon shauki, fito da abubuwa fili da kima mutuntawa na mahalarta taron, da hakan zai taka rawa sosai wajen tabbatar da cewa jihar ta kafa tare da gudanar da shirye-shirye masu inganci da dorewa da don kai matakin lafiya da duniya ke tafiya a kai.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
