Connect with us

News

Hukuncin Da Muka Zartar Na Korar Gwamnan Kano Na Nan Daram – Kotu

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta yi ƙarin haske a kan ce-ce-ku-cen da ake yi kan kundin hukuncin da ta zartar da ya kori Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, daga kujerarsa a ranar Juma’a.

Advertisement

Kotun dai a hukuncinta na ranar Juma’a ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zabe ta yi na soke nasarar Abba na jam’iyyar NNPP tare da maye gurbinsa da Nasiru Yusuf Gawuna na APC.

Shugaba Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Kai Ziyara Saudiyya Da Guinea Bissau

Sai dai kwafin kundin hukuncin da ya bayyana ranar Talata na cike da ruɗani kuma ya janyo ce-ce-ku-ce matuka.

Advertisement

To sai dai da yake ƙarin haske a kan ka-ce-na-cen, Babban Magatakardar kotun, Umar Mohammed Bangari, ya ce abin da ya jawo matsalar tuntuɓen alkalami ne.

 

Advertisement

Ya kuma ce hakan ba zai canza hukuncin da alkalai suka sanar da murya ɗaya ba, wanda ya tabbatar da matsayin kotun ta baya.

 

Advertisement

Umar Bangari ya kuma ce za a gyara kuskuren da zarar ɓangarorin da shari’ar ta shafa suka bukaci yin hakan a rubuce.

Bugu da kari, ya jaddada cewa doka ta hudu a ɗaftari na 23 na kotun ta ba su damar yin gyara a kan duk wani tuntuben alkalamin da suka ankare ko kuma ɗaya daga cikin bangarorin da suke ƙara suka ankarar da su.

Advertisement

Ya ce saɓanin kururuwar da ake yi a kafafen sada zumunta, har yanzu soke nasarar Abban da suka yi tana nan daram.

Ya ce, “Abin da ya faru a wani ɓangare na hukuncin wani tuntuɓen alkalami ne da bai kamata ya jawo wani ka-ce-na-ce ba.

Advertisement

“Kotun na da damar gyara duk wani kuskure da aka lura da shi. Kuka za mu yi hakan a kan lokaci,” in ju Umar Bangari.

A wani labarin kuma, tuni Gwamna Abba ya garzaya Kotun Koli inda yake neman ta yi watsi da hukunce-hukuncen kotunan guda biyu.

Advertisement

A wani labarin kuma Shugaba Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Kai Ziyara Saudiyya Da Guinea Bissau

Wata babbar kotu a Isra’ila ta kori ƙarar da aka shigar gabanta da ke ƙalubalantar yarjejeniyar da Isra’ila da Hamas suka ƙulla ta tsagaita wuta ta kwana huɗu.

Advertisement

Yarjejeniyar za ta fara aiki da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar gobe Alhamis agogon Gaza. Ta tanadi cewa Isra’ila za ta saki fursunonin Falasɗinawa 150 da take tsare da su, akasari mata da matasa. Hamas kuma ta saki Isra’ilawa 50 cikin kwana huɗu.

Kotun ta ce yarjejeniyar ta siyasa da diplomasiyya ce. ‘Yan uwan waɗanda Hamas ta kashe ne a harin da ta kai a watan da ya gabata suka shigar da ƙarar.

Advertisement

Masu ƙarar sun ce sakin fursinonin Falasdinawa zai iya janyo ƙaruwar kai hare-hare nan gaba.

Wakiliyar BBC ta ce an iya gano 34 daga cikin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su wadanda matasa ne ƴan ƙasa da shekara 18 kuma cikinsu har da yaro dan kasa da shekara ɗaya da haihuwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending