Connect with us

News

Daya daga cikin riƙaƙƙun ‘yan daba a jihar Kano, ya miƙa kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Hantar Daba, ɗaya daga cikin riƙaƙƙun ‘yan daba a jihar Kano, ya miƙa kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar.

A cewar ‘yan sandan, Hantar Daba yana da yara ‘yan daba kimanin 100 a karkashinsa, kuma ya yi alkawarin shawo kansu su ma su kai kansu don ajiye makamai tare da rungumar turbar zaman lafiya.

Advertisement

Hukumar EFCC ta fitar da matakai takwas na kare kai daga masu damfara da katin ATM

A baya dai, ƴan sandan sun sanya tukwicin naira dubu ɗari biyar a kan wasu ‘yan daba uku, ciki har da Hantar Daba.

Wannan mataki dai na daga cikin kudurin rundunar ‘yan sandan na dakile ayyukan ‘yan daba a faɗin jihar.

Advertisement

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a yau Talata.

Sanarwar ta ce “Hantar Daba, tare da rakiyar mahaifiyarsa da ’yan uwa, ya nuna nadamar abin da ya aikata a baya tare da nuna aniyarsa ta shiga shirin gwamnatin jihar na afuwa.”

Advertisement

“Mika wuyan ya zo ne bayan wani sauyin tunani da aka samu yayin wani taro na baya-bayan nan a filin wasa na Sani Abacha a ranar 17 ga Oktoba, 2023.”

Tuni dai Abba Burakita da Chile Maidoki, sauran ƴan daban biyu da aka saka tukuici a kansu suka miƙa wuya ga ƴan sandan jihar.

Advertisement

Yanzu haka, Hantar Daba yana hannun ‘yan sanda, kuma ana tantance al’amuran tsaro da suka shafe shi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel, ya yaba wa ƙoƙarin al’umma, ya kuma buƙaci duk wanda ke da korafi kan Hantar Daba da ya fito

Advertisement

Bbc ta ruwaito cewa Ya kuma ja hankalin jama’a da su kai rahoton duk wani abu da ake zargi na rashin tsaro ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma ta hanyar lambobin tuntuɓar gaggawa da kafofin watsa labarai na intanet.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending