Connect with us

News

Kotun Daukaka Kara Ta Soke Zaben Mataimakin Kakakin Majalisar Bauchi

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Kwanaki kadan bayan soke zaben kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja, ta sake soke zaben mataimakin kakakin majalisar, Jamilu Umaru Dahiru Barade na jam’iyyar PDP.

Advertisement

Kotun mai Alkalai guda uku, a hukuncin da ta yanke a ranar Litinin din da ta gabata, sun yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, wadda tun farko ta tabbatar da zaben Barade a matsayin zababben dan majalisa mai wakiltar mazabar Bauchi ta tsakiya.

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun soke dokar da ta haramta tafiya ci-rani

Don haka, alkalan sun bayar da umarnin sake gudanar da zabe a wasu rumfunan zabe na mazabar, inda mai shigar da kara na jam’iyyar APC, Aliyu Abdullahi Ilela, ya yi zargin cewa an yi aringizon kuri’u.

Advertisement

Leadership ta ruwaito cewa Kotun ta umurci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta karbo takardar shaidar cin zabe da aka baiwa mataimakin shugaban majalisar tare da sake gudanar da zabe a rumfunan zaben da abin ya shafa kafin sake tantance wanda ya yi nasara.

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Hukuncin ya zo ne kwanaki kadan bayan da kotun daukaka kara ta soke zaben Kakakin Majalisar, Abubakar Sulaiman.

Advertisement

A wani labarin kuma Sojojin Jamhuriyar Nijar sun soke dokar da ta haramta tafiya ci-rani

An fara shari’ar matar tsohon shugaban kasar Zambia Esther Lungu, matar tsohon shugaban kasa Edgar Lungu a birnin Lusaka.

Advertisement

Ana tuhumar ta ne da laifin satar motoci uku, da satar wani kadarori a Lusaka da kuma mallakar dala 400,000 da ake zargin ta samu ne ta aikata laifi.

Ana tuhumar ta ne tare da wasu ‘yan sanda biyu.

Advertisement

Wani shaida ya shaida wa kotu a ranar Litinin cewa Lungu ta ƙwace motarta da karfin tsiya da takardar mallakar gidanta da kuma motoci biyu na ‘yarta.

Ta kara da cewa jami’an ‘yan sandan da ake zargi sun tilasta musu sanya hannu kan takardun kadarorin ga Lungu.

Advertisement

Lungu da wadanda ake tuhumarsu tare sun musanta aikata ba daidai ba lokacin da aka kama su kan laifukan da ake zarginsu da aikatawa a watan Satumba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending