Connect with us

News

Yawan Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Haura Sama Da  Tiriliyan 87

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Yawan bashin da ake bin Najeriya a Kasashen waje zai kai sama da dala biliyan 51 da milyan 759, yayin da a jiya ne shugaban kasa Bola Tinubu ya nemi amincewar majalisar dokoki ta kasa, domin karbo sabon lamunin dala biliyan 8 da milyan 6 da kuma Euro miliyan 100 daga kasashen waje.

Bukatar Shugaban kasar wani bangare ne na basussukan da za’a ciwa daga kasashen daga shekarar 2022 zuwa 2024 domin gudanar da muhimman aiyukan raya kasa, kamar wutar lantarki da samar da hanyoyi da inganta samar ruwa da shimfida layin dogo da kuma bunkasa fannin kiwon lafiya.

Advertisement

Kotun Koli Ta Ce A Ci Gaba Da Amfani Da Tsoffin Takardun Kudi Har Sai Sabin Da Hali Ya Yi

A cewar ofishin kula da ciwo basussuka na kasa, yawan bashin da ake bin kasar nan zuwa watan Yunin da ya gabata, ya kai dala biliyan 43 da milyan 159, yayin da bashin cikin gida ya kai Naira tiriliyan 54 da bilyan 130.

Zuwa yanzu jimillar bashin da ake bin Najeriya na cikin gida da kasashen waje ya kai Naira tiriliyan 87 da bilyan 379.

Advertisement

A wani labarin kuma Kotun Koli Ta Ce A Ci Gaba Da Amfani Da Tsoffin Takardun Kudi Har Sai Sabin Da Hali Ya Yi

Magoya bayan jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano su na ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana kan abin da suka kira ƙoƙarin murɗe musu zaben gwamnan jihar.

Advertisement

Wannan na zuwa ne bayan da kotun ɗaukaka ƙara ta soke zaben gwamna Abba Kabir Yusuf.

A waje daya kuma rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayar da umarnin kama wani jami’inta da ake zargi da bude wuta kan wasu matasa unguwar Kurna abin da yayi sanadin mutuwar mutum guda lamarin da ya janyo matasan suka gudanar da zanga-zanga

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending