Connect with us

News

Gwamnan Jahar Ogun Ya Gabatar Da Kasafin Kudin Naira Biliyan 703

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 na Naira biliyan 703.028 ga majalisar dokokin jihar.

Kasafin kudin 2024 da aka gabatar ya zarce na 2023 na Naira biliyan 472.250 da Naira biliyan 230.78.

Advertisement

Kotun daukaka kara Tace Zaɓen Dan Majalisar Kunchi/Tsanyawa Bai Kammala ba

A cikin kasafin kudin,ababen more rayuwa zasu lakume makudan kudade,na Naira biliyan 209,122.60, wanda ke wakiltar kashi 30 cikin 100 na abin da aka ware.

An gabatar da kudirin kasafin ne a gaban majalisar dokokin jihar karkashin jagorancin kakakin majalisar, Olakunle Oluomo, a harabar majalisar dake Oke-Mosan, Abeokuta, babban birnin jihar.

Advertisement

Abiodun ya ce za a samar da kasafin ne da kudaden shiga na cikin gida (IGR), wanda aka kiyasta ya kai Naira biliyan 100.81 da kuma kaso na doka daga Gwamnatin Tarayya da aka kiyasta ya kai Naira biliyan 182.05 da dai sauransu.

Gwamnan ya sanya kasafin kudin shekarar 2023 zuwa kashi 74.39 bisa 100, inda ya kara da cewa gwamnatinsa za ta karkata akalar tattalin arzikin jihar ta hanyar hako ma’adinai.

Advertisement

Daily Post ta ruwaito cewa Da yake jawabi ga ‘yan majalisar, gwamnan ya ce an ware naira biliyan 415.66 a matsayin babban jari, yayin da aka ware naira biliyan 287.37 a matsayin kudaden da ake kashewa akai-akai.

A wani labarin kuma Kotun daukaka kara Tace Zaɓen Dan Majalisar Kunchi/Tsanyawa Bai Kammala ba

Advertisement

Hamas ta yi ikirarin cewa mayakanta ne suka kaddamar da harin Birnin Kudus da safiyar yau, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku, kamar yadda kungiyar ta wallafa a shafinta na Telegram.

Cikin sanarwar, Hamas ta ce ”ta kai hari ne saboda mayar da martani kan laifukan da ake aikata wa al’umominta ta hanyar mamaya,” tana mai kafa hujja da ayyukan sojin Isra’ila a Gaza da yadda ta ce ana muzgunawa Falasdinawa a gidajen yarin Isra’ila.

Advertisement

Kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ambato sanarwar kungiyar na kira ga mambobinta da su ”ci gaba da fadada juriya”.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending